13 Mayu 2015 - 10:49
Yan bindiga sun kaima motar mabiya Shi’a isma'iliya hari a Karachi Pakistan

Wasu ‘Yan bindiga sun bude ma wata mota kirar Bus wuta da ke dauke da mabiya Shi’a isma'iliya idan mutane sama da 43 sukayi shahada wasu 13 suka jikkata a birnin Karachi na kasar Pakistan a yau Laraba. ‘Yan bindiga guda shida ne suka bude ma Motar wuta da karamar Bindiga bayan sun zo saman babura, kamar yadda ‘Yan sandan Pakistan suka tabbatar.

An bayyana harin a matsayin mafi muni tun harin da aka kai a watan Janairu inda wani dan kunar bakin wake ya danama  kansa Bom a wani masallaci da ke kudancin Shikapur tare da kashe mutane 61.

Pakistan dai na fama da matsalar rikicin babbancin akida, musamman yanda 'yan ta'adda ke kaima  mabiya shi’a har-har a kasar mai yawan musulmi Miliyan 200.ABNA